Hernandez zai yi jinyar makwanni biyu

Javier Hernandez
Image caption Javier Hernandez

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce dan kwallonsa Javier Hernandez zai yi jinyar makwanni biyu.

Dan wasan Mexico din mai shekaru 23 ya jimu ne lokacin horo a New Jersey kafin wasan sada zumunci tsakanin United da hadakar 'yan kwallon Amurka.

Ferguson yace "ya samu 'yar matsala lokacin muna horo amma kuma sai aka kaishi asibiti".

A cigaba da rangadi a Amurka din ,united za ta fuskanci Barcelona a ranar asabar sanan ta kara da New York Cosmos a ranar biyar ga watan Agusta kafin ta kara da Manchester City a wasan Community Sheild.

Hernandez ya ciwa United kwallaye 13 a gasar Premier tun zuwansa daga kungiyar Chivas de Guadalajara ta Mexico akan fan miliyon bakwai.