Dan Barca Afellay zai jinyar makwanni biyar

Ibrahim Afellay Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahim Afellay

Dan kwallon Barcelona Ibrahim Afellay zai yi jinyar makwanni hudu zuwa biyar saboda rauni a cinyarsa.

Dan wasan Holland din mai shekaru 25 wanda ya koma Barca daga PSV Eindohoven a watan Disamba ya jimu ne a wasan da Barcelona ta sha kashi a wajen Manchester United a Washington DC a ranar Asabar.

Sanarwar da Barcelona ta fitar ta ce "mun tabbatar da raunin Ibrahim Afellay kuma likitocinmu sun ce zai shafe makwanni hudu zuwa biyar baya taka keda".

Kenan bai zai buga wasan Spanish Supercup tsakaninsu da Real Madrid a ranakun 14 da 17 ga watan Agusta sai kuma na European Supercup tsakaninsu da Porto a ranar 26 ga watan Agusta.