Muna sha'awar Juan Mata a Spurs-Redknapp

Juan Mata.
Image caption Juan Mata

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya tabbatar da cewa yanada sha'awar sayen dan kwallon Valencia Juan Mata.

Mata mai shekaru 23 anata bada rahotanni cewar zai bar kulob din ya koma Spurs ko kuma Arsenal.

Redknapp yace"Mata dan wasa ne da muke so, kuma yayi murza leda".

Ya kara da cewar "shugabanmu na tattaunawa akan batun sa saboda ni bani da hannu akai".

Idan har Mata ya koma Spurs, akwai alamun cewar Luka Modric zai iya barin kulob din zuwa Chelsea.