Chelsea zata bada tayin Modric aka na uku

modric Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric

A wannan makonne Chelsea zata yanke shawara akan batun sake bada tayi akan dan kwallon Tottenham Luka Modric.

Shugaban kulob din Ron Gourlay zai tattauna da sabon kocin kulob din Andre Villas-Boas akan yiwuwar bada tayi a karo na uku akan Modric.

Rahotanni sun nuna cewar Modric ya baiwa Spurs takarda a rubuce akan cewar yanason barin kulob din.

Chelsea ta bada tayi har sau biyu akan Modric mai shekaru 25 wato tayin farko na fan miliyon 22 na biyu kuma fan miliyon 27.

Baya ga Modric, Chelsea na zawarcin dan kwallon Palermo Javier Pastore da kuma dan wasan Anderlecht Romelu Lukaku.