Manchester United ta doke Barcelona a Amurka

fargie/guadiola
Image caption Sir Alex Ferguson da Pep Guardiola

Micheal Owen ya zira kwallo daya a wasan da Manchester United ta doke zakarun kwallon Turai Barcelona daci biyu da daya a wasan sada zumuncin da suka buga a Washington DC.

A wasan da 'yan kallo dubu 82 suka cika fili, Nani ne ya fara ciwa United kwallon farko a minti na 22.

Barcelona banda Lionel Messi a cikin wasan, ta farko ne a minti na 70 inda Thiago Alcantara yaci kwallon.

Sakamakon wannan wasan ya nuna cewar United ta samu nasara a karawarta biyar cikin biyar a rangadin data yi zuwa Amurka.

Za a iya cewa United ta farke kashin data sha a wajen Barcelona a wasan karshe na gasar zakarun Turai a filin wasa na Wembley a watan Mayu.

A yanzu dai yaran Sir Alex Ferguson zasu koma gida don haduwa da Manchester City a ranar Lahadi a wasan Community Shield.at Wembley.