Najeriya ta lallasa Guatemala da ci biyar

Image caption 'Yan wasan Najeriya

Najeriya ta lallasa Guatemala da ci biyar da nema a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 20 wadda aka buga a ranar lahadi.

Dan wasan Najeriya Edafe Egbedi ya zura kwallaye biyu a wasan.

Egbedi ya zura kwallon farko ne ana minti takwas da wasa sannan ya kara ta biyu ana minti 39, a wasan da aka fafata a rukunin D.

Abdul Ajagun ya zura ta uku ana minti 47, sai Olarenwaju Kayode da ya zura ta hudu ana Minti 53.

Ahmed Musa ne dai ya zura kwallon karshe ana minti 76 da wasan.

Gasar da Najeriya din ta halarta shine karo na takwas, kuma kasar bata taba lashe gasar ba.

A ranar laraba, Najeriya za ta kece raini da Croatia, sai kuma Guatemala da za ta kara da Saudi Arabia.