Antonio Valencia ya sabunta kwantiragi da United

Antonio Valencia
Image caption Antonio Valencia ya yi fama da rauni

Dan wasan Manchester United Antonio Valencia ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da kulob din ta tsawon shekaru hudu har zuwa shekara ta 2015.

Dan wasan mai shekaru 25 ya zira kwallaye 10 a wasanni 69 da ya buga tun bayan zuwansa United daga Wigan Athletic a shekara ta 2009.

Ya shaida wa shafin intanet na kulob din cewa: "Na yi farin cikin ci gaba da zama a United. Ina fatan zan ci gaba da haskakawa.

"Ina fatan bayar da gudummawata wajen ganin wannan kulob din ya lashe kofuna da dama a nan gaba."

Dan wasan na kasar Ecordor ya yi fama da matsalar rauni a baya.

Amma kociya Alex Ferguson ya bayyana farin cikinsa kan sabuwar yarjejeniya da dan wasan. "Antonio ya taimaka mana sosai matuka tun bayan zuwansa. Saurinsa da yadda yake buga kwallo ya taimaka mana kwarai da gaske," a cewa Ferguson.