Brazil na neman buga wasan wasan sada zumunci da Ingila

Image caption Ingila da Brazil na fafatawa

Akwai yiwuwar Ingila ta buga wasan sada zumunci da Brazil, a wani bikin na bude daya daga cikin filayen wasan da za'a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 2014.

Ana dai kara inganta filin wasa na Mineirao ne dake Belo Horizonte, kuma za'a kammala gyaran filin wasan ne a shekarar 2013, kuma sakataren gwamnatin lardin ya ce yana ganin Ingila ce kasar farko da ya kamata a fafata da ita a filin wasan.

Sergio Barroso ya ce: "Muna son Ingila ta buga wasan sada zumunci da Brazil a bikin bude sabon filin wasan."

Wasan karshe da Ingila ta buga a Belo Horizonte, shine wanda ta sha kashi a hannu Amurka da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka buga a shekarar 1950.