Usain Bolt na son komawa kwallon kafa

Image caption Usain Bolt

Shahararen dan tseren gajeren zangon nan Usain Bolt ya ce yana son komawa taka leda idan ya bar tsere.

"Da gaske nake, na yi imanin zan iya zama dan kwallon kafa, kuma zan taka rawar gani." In ji Bolt.

Dan tseren mai shekarun haihuwa 24 ya ce da kamar wuya ya buga a wata babbar kungiya, amma bai cire rai ba wata babbar kungiya za ta nemi ya buga mata.

Ya ce yana ganin nan gaba zai rika bugawa a wasu wasanni tara kudin agaji daga nan zai ya zarce harkar kwallon kafa gadan-gadan.

Usain Bolt dai ya buga kwallon kafa a lokacin da yake makarantar sakandare, kuma ya buga ta tsakiya ne.