Jerin 'yan wasan Ghana da za su buga da Najeriya

Kocin Ghana, Goran Stevanovic ya fito da jerin sunayen 'yan wasa 18 da za su buga wasan sada zumunci da Najeriya a ranar Talata mai zuwa.

Kasashen biyu za su buga wasan ne a matsayin share fage, kafin wasanni cancantar taka leda na gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2012 da za su buga.

Jerin sunayen 'yan wasan

Masu tsaron gida: Richard Kingson da Adam Larsen Kwarasey

'Yan wasan baya: John Mensah da Nana Akwasi Asare da John Paintsil da Samuel Inkoom da Jonathan Mensah da Isaac Vorsah da kuma Daniel Opare

'Yan wasan tsakiya: Anthony Annan da Emmanuel Agyemang-Badu da Andre Ayew da Mohammed Rabiu da Sulley Muntari da kuma Kwadwo Asamoah

'Yan wasan gaba: Asamoah Gyan da Prince Tagoe da kuma Dominic Adiyiah