Martin Atkinson ne zai jagoranci wasan Najeriya da Ghana

Image caption Martin Atkinson

Alkalin wasan Ingila Martin Atkinson ne zai jagoranci wasan sada zumuncin da Najeriya za ta buga da Ghana a ranar talata mai zuwa a Watford.

An zabi alkalin ne mai shekarun haihuwa 40, domin ya jagoranci wasan wanda za'a buga a Ingila a ranar 9 ga watan Agusta.

Alkalan wasa Peter Kirkup da Stuart Burt da kuma Rob Shoebridge ne za su taimaka masa.

Atkinson ne ya hura wasan karshe na gasar cin kofin FA da kungiyar Manchester City ta lashe a bara.

Shine kuma ya jagoranci wasan da Chelsea ta doke Manchester United da ci 2-1 a filin Stamford Bridge, wasan kuma da kocin United Sir Alex Ferguson ya yi korafi akai, inda ya ce alkalin wasan ya ba Chelsea fenaritin da bai kamata ba.