Eric Cantona ya kare birnin Manchester

Eric Cantona Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Eric Cantona ya taka leda sosai a United

Tsohon dan wasan Manchester United Eric Cantona ya kare birnin Manchester na Ingila, bayan da Carlos Tevez da Mario Balotelli an Man City suka soka ce birnin ba ya burgesu.

Cantona na magana ne a daidai lokacin da 'yan wasan Manchester City Carlos Tevez da Mario Balotelli suka ce suna kewan gida domin rashin jin dadin zamansu a birnin.

Eric Cantona ya ce muhimmin abu shi ne na buga kwallon kafa.

Yace ni lokacin da nake Manchester, na ji dadin zama domin buri na kawai shi ne na taka leda, kuma na zamo daya daga cikin kwararrun 'yan wasa a duniya.

Su dai 'yan wasan na Man City sun ce ba sa jin dadin zama a birnin ne saboda yana da karancin ababen more rayuwa, kuma suna kyawar iyalansu.