Chelsea ta sayi Romeu daga Barcelona

Oriol Romeu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oriol Romeu zai bunkasa tsakiyar Chelsea a rashin Essien

Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya Oriol Romeu daga Barcelona inda yasa hannu a kwantiragin shekaru 4 a kan fan miliyan 4 da doriya.

Romeu zai isa Stamford Bridge ne da zarar ya kammala taka wa Spain leda a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 da ake yi a kasar Colombia.

Dan wasan mai shekaru 19 ya buga duka wasannin da Spain ta yi inda ta doke Costa Rica da ci 4-1, sannan ta doke Ecuador da ci 2-0.

Dan wasan dai ya taba buga wa babbar tawagar Barcelona wasa sau biyu, amma ba ya cikin shirin koci Pep Guardiola.

Romeu, ya bayyana Chelsea da cewa "babban kulob ne," kuma ba karamin zabi ba ne a gare ni," a cewarsa.

"Da tsauri barin Barca, amma dole ne mutum ya yi amfani da damarsa."