Arsenal za ta tattauna da Barca kan Fabregas

Cesc Fabregas
Image caption A yanzu ance Cesc Fabregas yana fama da rauni

Shugaban Arsenal Ivan Gazidis zai gana da jami'an Barcelona a ranar Juma'a kan makomar kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas.

BBC ta fahimci cewa har yanzu Arsenal bata samu wani tayi ba, bayan na fan miliyan 27 da Barca ta gabatar a watan da ya gabata.

Sai dai kulob din na da niyyar sayar da dan wasan idan har Barcelona ta iya biyan fan miliyan 40 da suka nema.

Mutumin da ya fi kowa hannun jari Stan Kroenke ba zai halarci tattaunawarba saboda ya tafi gida Amurka bayan ziyarar da ya kai Emirates ranar Alhamis.

Shekaru biyu kenan ana danganta Fabregas da komawa Nou Camp, inda ya fara taka leda tun yana dan shekara 10.

An takurawa dan wasan na Spain sanya jesin Barcelona a lokacin da Spain ke murnar lashe gasar cin kofin duniya bara.

Fabregas bai halarci horon da Arsenal ke yi a Jamus da kuma nahiyar Asia ba, inda aka ce yana fama da rauni.