Tottenham za ta kara da Hearts a Europa

Tottenham za ta kara da Hearts a Europa Hakkin mallakar hoto a
Image caption Bara Tottenham ta taka rawar gani a gasar cin kofin zakarun Turai

Tottenham za ta fafata da Hearts na Scotland a wasan share fage na shiga gasar cin kofin Europa League.

Zakarun gasar Scotland Rangers za su kara da Maribor na Slovenia yayin da Celtic za ta fafata da Sion na Switzerland.

Zakarun gasar Carling an Ingila Birmingham, wadanda suka fada gasar Championship, za su hadu da Nacional na Portugal, sai kuma Fulham da za ta fafata da Dnipro na Ukraine.

Stoke City za ta kece raini ne da FC Thun na Switzerland.

Fulham ta zo wannan matsayin ne bayan da ta doke RNK Split na Croatia da ci 2-0.