Wenger ne yafi dacewa da Arsenal-Dein

David Dein da Arsene Wenger
Image caption David Dein da Arsene Wenger

Tsohon mataimakin shugaban Arsenal David Dein yace Arsene Wenger shine wanda yafi dacewa da kasancewa kocin Gunners.

Arsenal bata lashe kowanne kofi ba tun shekara ta 2005 kuma akwai matsin lamba akansa matuka saboda rashin nasara a Emirates.

Dein wanda yake cikin na gaba gaba da suka sanya akan nada Wenger a shekarar 1996, ya shaidawa BBC "ya kamata mutane su tuna irin nasarorin da suka cimma".

Dein wanda ya fice daga Arsenal a shekara ta 2007 ya ce har yanzu yana dasawa da Wenger.

Kawo yanzu dai Arsenal ta siyo Gervinho da Carl Jenkinson a kasuwar musayar 'yan kwallo kuma tana zawarcin dan wasan Everton Phil Jagielka.