PSG ta siyo Pastore akan fan miliyon 37

Javier Pastore Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Javier Pastore

Dan kwallon Palermo Javier Pastore ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar Paris Saint-Germain ta Faransa.

PSG ta sayi dan kwallon Argentina din mai shekaru 22 akan fan miliyon 37 kuma ya kasance dan wasa na takwas da kulob din ya siyo a kwananan.

A halin yanzu dai PSG ta kashe kusan fan miliyon 73 akan 'yan wasa tun bayan da kamfanin Qatar Investment Authority ya siyi kulob din.

Pastore ya bugawa Palermo wasanni 35 a kakar wasan data wuce inda ya zira kwallaye 11.