Alex Oxlade ya kammala gwaji a Arsenal

Alex Oxlade-Chamberlain Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oxlade-Chamberlain shi ne na uku da Arsenal ta dauka a bana

Dan wasan gefe na Southampton Alex Oxlade-Chamberlain ya kammala gwajin lafiya a kan hanyarsa ta komawa Arsenal.

Ana saran kammala cinikin nan gaba a ranar Litinin ko Talata, inda Oxlade-Chamberlain zai sanya hannu kan doguwar kwantiragi a Emirates.

Duka Arsenal da Southampton ba su bayyana farashin cinikinba, amma ana saran zai kai fan miliyan 12.

Dan wasan na tawagar 'yan kasa da shekaru 21 ta Ingila mai shekaru 17, zai zamo dan wasa na uku da koci Arsene Wenger ya dauka anan gaba.

A baya ya dauki Carl Jenkinson daga Charlton da kuma Gervinho daga Lille.