An sa ni a kasuwa - In ji Sneijder

Image caption Wesley Sneijder

Dan wasan tsakiya na kulab din Inter Milan Wesley Sneijder ya ce dole ne a saye shi da daraja a yayin da aka zo sayensa.

Dan wasan, wanda shi ne ya taimaka wa kasar Netherlands ta kai ga zagayen karshe na gasar kwallon duniya da aka gudanar a Afrika ta Kudu a shekarar 2010, ya ce bai tattauna da kulob din City da United ba, don haka ba zai ce komai ba game da yiwuwar komawarsa daya daga cikinsu.

Ya shaidawa mujallar Voetbal International cewa zai bugawa kulob din Oranje wasa wanda za su yi da Ingila a makon gobe, inda daga bisani zai samu hutu na kwanaki biyar, kuma bayan haka ne zai san matsayinsa.

Akwai dai jita-jitar cewa Sneijder zai koma daya daga cikin kulob biyu wato Manchester United ko City, sai dai jami'an kulob din sun musanta cewa akwai yarjejeniya tsakaninsu da dan wasan.