Tevez ya koma horo da Man City

Carlos Tevez
Image caption Carlos Tevez ya ce yana kyawar iyalansa ne

Carlos Tevez ya koma horo da Manchester City ranar Litinin kamar yadda aka tsara, a yayin da ake ci gaba da nuna shakku kan makomarsa a kulob din.

Dan wasan na kasar Argentina, wanda ya yi hutun kwanaki 21 bayan kammala gasar cin kofin Copa America, ya isa filin horon ne kafin karfe goma na safe.

Tevez, mai shekaru 27, bai taka leda a wasan da City ta sha kashi da ci 3-2 a hannun Manchester United ba a gasar Community Shield ranar Lahadi.

Yunkurinsa na komawa Corinthians a kan fan miliyan 40 ya ci tura a watan Yuli, amma wakilinsa Kia Joorabchian ya ce har yanzu dan wasan na son barin Man City.

Wakilin BBC David Ornstein, ya ce dan wasan ya fita filin horon ne da wuri, sabanin yadda aka yi tsammani tare da Pablo Zabaleta da kuma kocin da ke kula da lafiyar 'yan wasa."