Chamberlain ya kulla yarjejeniya da Arsenal

Oxlade-Chamberlain Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oxlade-Chamberlain

Arsenal ta kulla yarjejeniya da dan wasan Southampton Alex Oxlade-Chamberlain akan fan miliyon 15.

Dan wasan mai shekaru 17 ya koma Gunners a kwangilar da zai shafe shekaru da dama tare da ita.

Chamberlain ya zira kwallaye 10 a cikin wasanni 41 daya buga Southampton.

Kocin Gunners Arsene Wenger ya ce "Muna jiran cin gajiyarsa yadda ya dace".

Southampton ta bayyana cewar wannan cinikin shine yafi kowanne tsoka a tarihin kulob din bayan musayar Theo Walcott zuwa Arsenal a shekara ta 2006 akan fan miliyon 12.

Oxlade-Chamberlain ya kasance dan kwallo na uku da Wenger ya siyo a kwanan nan bayan Carl Jenkinson daga Charlton da kuma Gervinho daga Lille.