An dage wasan Najeriya da Ghana na London

Nigeria Ghana Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya da Ghana manyan abokan hammaya ne

Sakamakon tashin hankalin dake gudana a London, an dage wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Ghana wanda ya kamata su buga a ranar Talata a filin Watford Vicarge Road.

Haka kuma an fasa buga wasu wasanni kofin Carling da kuma wasan sada zumunci tsakanin Ingila da Netherlands wanda ya kamata a buga a filin Wembley.

Mahukunta a Watford inda za ayi wasan sunce ba zasu iya tabbatar da tsaro ba.

Jami'an 'yan sanda a wasu yankunan Birtaniya an hadasu cikin 'yan sandan birnin London don kwantar da hankali.

Tun da farko dai wadanda suka shirya wasan sunce za a buga wasan tsakanin Ghana da Najeriya duk da zanga zangar da ake yi a London, amma daga bisani hukumar kwallon Ghana GFA ta tabbatar da cewar ba za a buga wasan ba.

Jami'in hukumar GFA Randy Abbey ya ce"wadanda suka shirya gasar sun bayyana mana cewar an fasa wasanmu da Najeriya da ya kamata a buga a Watford".