Dan United Bebe zai yi jinyar watanni shida

Bebe

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Bebe

Dan kwallon gefe a Manchester United Bebe zai yi jinyar watanni shida saboda rauni, wato kenan sai a watan Fabarairu zai komo taka leda.

Bebe yaji ciwo a gwiwarsa ne a wasan daya bugawa Portuga a karawatta da Slovakia a matakin 'yan kasada shekaru 21.

Dan wasan maishekaru 21 wanda aka badashi aro zuwa Besiktas, kenan ba zai samu damar bugawa a kulob din.

Likitan kulob din Besiktas Devrim Uygun ya ce"An dauki hoton kafarsa ta hagu kuma ba zai iya taka leda ba na watanni shida".

Ya kara da cewar ana bukatar tiyata dole ne kuma sai United da Besiktas sun amince sannan ayi fidar.

Akwai yiwuwar United ta fasa badashi a matsayin aro don ya koma Old Trafford yayi jinyar acan.