Anzhi ta bada tayi 'mai tsoka' akan Eto'o

etoo
Image caption Samuel Eto'o

Shugaban Inter Milan Massimo Moratti na kokwanto akan tayi "mai tsoka" akan dan kwallon Kamaru Samuel Eto'o.

Kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha wacce ke kashe makudan kudade akan 'yan kwallo, tana zawarcin Eto'o ya bara gasar Serie A.

Wakilin Eto'o Claudio Vigorelli, ya bayyana cewar an kusan kamalla yarjejeniya tsakanin dan wasan da Anzhi.

Rahotanni sun nuna cewar kulob din na Rasha zai bada akalla dala miliyon 30 zuwa 40 akan Eto'o.

Moratti yace" Akwai tayi me kyau akan darajar dan kwallon".

Sai dai Inter na kokarin sayarda Eto'o don ta samu damar siyo dan kwallon Manchester City Carlos Tevez.

Anzhi ta riga ta siyo dan Brazil Roberto Carlos da dan Rasha Yuri Zhirkov daga Chelsea.

Attajirin dan kasuwa mai arziki a fannin mai da karafa Suleiman Kerimov shine keda Anzhi Makhachkala.