Na soma tattaunawa da United-Sneijder

sneijder
Image caption Wesley Sneijder

Dan wasan Inter Milan Wesley Sneijder ya ce watakila ya koma Manchester United saboda ya soma tattaunawa da kulob din a bayan fage.

Dan kwallon mai shekaru 27 an dade ana alakantashi da komawa Old Trafford kuma yace idan aka bada kudaden da suka dace zai koma.

A watan Yuli, Kocin United Sir Alex Ferguson ya karyata batun zawarcin Sneijder, sannan Inter ta ce United bata tuntubeta akan dan kwallon Holland din ba.

Sneijder yace"A halin da ake ciki a yanzu, ni dan wasan Inter ne amma akwai alamun zan bar kulob din".

Sannan ya kara da cewar Inter ta bayyana cewar idan aka bada farashin daya dace zasu barni in tafi.