'Yan kwallon gasar Spain zasu yi yajin aiki

laliga Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan wasan Barcelona

Watakila a dage wasannin gasar Spain a karshen mako saboda kungiyar 'yan kwallon gasar ta kira yajin aiki.

'Yan kwallon na bukatar a tabbatar musu da cewar za a din biyansu albashinsu koda kuwa kulob ya durkushe, a don haka akwai ta baba akan wasanni na makwanni biyu masu zuwa.

Shugaban kungiyar 'yan kwallon Luis Rubiales yace"Wannan shawara ce tya bai daya, kuma ba za a fara gasar ba sai an sanya hannu a yarjejeniyar"

A ranar 21 ga wannan watan ne ya kamata a fara gasar La Liga na kakar wasa ta bana.

A baya kungiyar Hercules da kyar ta biya albashin 'yan kwallonta, sannan kuma Real Zaragoza ta durkushe.

Shugaban kungiyar Luis Rubiales dai ya samu 'yan rufe baya kamarsu Iker Casillas na Real Madrid da Xabi Alonso da kuma Carles Puyol.