Bolton na zawarcin Wright-Phillips daga City

Shaun Wright-Phillips Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shaun Wright-Phillips

Kocin Bolton Owen Coyle ya ce kulob din na tattaunawa da dan kwallon Manchester City Shaun Wright-Phillips.

Dan kwallon Ingilan Wright-Phillips baya samun damar buga kwallo a karkashin Roberto Mancini kuma za a barshi ya tafi.

Sai dai matsalar itace alawus dinsa zai kasance irin na 'yan shekaru 30.

Coyle yace"Ya kasance wanda nake son in kawo kulob din".

Wright-Phillips yana fama da rashin tabbas a City saboda wasanni 10 kacal ya buga a kakar wasan data wuce.

Komawarsa Bolton zata taimakawa kulob din gannin cewar Lee Chung-Yong zai yi jinyar watanni tara saboda ya karya kafa.