West Brom na zawarcin Owen Hargreaves

Owen Hargreaves
Image caption Owen Hargreaves ya sha fama da rauni a rayuwar kwallonsa

West Brom ta yiwa tsohon dan wasan Manchester United Owen Hargreaves, wanda ke fama da rauni tayin komawa cikinta.

Kocin West Brom Roy Hodgson ya yi magana da dan wasan mai shekaru 30, kuma yana jiran martanin da Hargreaves zai mayar.

Daga nan ne kuma idan ya amince za a gwada lafiyarsa kafin sa hannu kan yarjejeniya.

Hargreaves na kokarin farfado da rayuwar kwallonsa ne bayan da Manchester United suka sallame shi.

Hodgson ya ce: "Ko bukatar ta mu za ta samu karbuwa ko kuma a'a - wannan shi ne abin da ban sani ba."

Hargreaves, wanda ya taka leda sau 42 a tawagar Ingila, ya buga wasanni 39 ne kacal a shekaru hudun da ya shafe a Old Trafford sakamakon raunin da ya yi ta fama da shi.