Chelsea ta tashi babu tsakaninta da Stoke City

torres Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Torres ya kasa zira kwallo

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas bai samu nasara ba a wasansa na farko a gasar Premier ta Ingila, bayanda Blues suka tashi babu ci tsakaninsu da Stoke a ranar Lahadi.

Yaran Villas-Boas din basuka taka rawar gani matuka kafin a tafi hutun rabin lokaci a filin wasa na Britannia, amma bayan an dawo hutun rabin lokaci, Chelsea ta kusa samun nasara ba domin golan Stoke Asmir Begovic wanda ya kabe kwallaye uku daga wucewa raga ba.

Kocin mai shekaru 33, ya kasance koci mafi karancin shekaru da aka nada a Chelsea bayan da Roman Abramovich ya nada shi a watan Yuli.

Chelsea ta kusa zira kwallo, amma sai Begovic ya kabe kwallon John Obi Mikel, kamar yadda kwallayen Nicolas Anelka da Salomon Kalou suka kasa wuce raga.