Bai kamata a kori Gervinho shi kadai ba-Wenger

gervinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gervinho da Barton sun 'cukwikwiye' juna.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai gane dalilan da suka sanya alkalin wasa Peter Walton ya kori Gervinho bayan yayi taho mu gama da dan kwallon Newcastle Joey Barton inda suka tashi babu ci a filin St James' Park.

Wenger na tunanin cewar kamata yayi Walton sya kori duka 'yan kwallon biyu ko kuma a baiwa dukansu katin gargadi.

Sakamakon sauran karawar da aka yi na gasar premier:

*Blackburn Rovers 1 - 2 Wolverhampton *Fulham 0 - 0 Aston Villa *Liverpool 1 - 1 Sunderland *Queens Park Rangers 0 - 4 Bolton Wanderers *Wigan Athletic 1 - 1 Norwich City *Newcastle United 0 - 0 Arsenal