Ba zan sayi karin 'yan kwallo ba-Mourinho

mourinho

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce ba zai kara siyo wani sabon dan kwallo ba a yayinda zai fuskanci babbar abokiyar hammayarsa Barcelona a wasan Super Cup a ranar Lahadi.

Mourinho ya siyo Hamit Altintop, Jose Maria Callejon, Fabio Coentrao, Nuri Sahin da Raphael Varane a kwanakin da suka wuce, kuma yace tawagarsa nada karfin lashe gasa a kakar wasan da aka soma.

Mourinho yace "bana bukatar wani sabon dan kwallon yazo nan, inada tawaga mai karfi".

Tsohon kocin Chelsea da FC Porto din ya ce fafatawarsu da Barca zai kasance mai zafi kamar yadda aka saba.