Manchester United ta soma da kafar dama

fergie
Image caption Sir Alex Ferguson

Manchester United ta soma gasar Premier ta Ingila da kafar dama bayan ta doke West Bromwich Albion daci biyu da daya.

Wayne Rooney ne yaciwa United kwallonta na farko kafin Shane Long ya farkewa West Brom.

Ana sauran minti tara a tashi wasan sai Steven Reid ya kansu bayan Ashley Yound ya bugo wata kwallo, abinda kuma ya baiwa United galaba a wasan.

Ita kuwa Chelsea ta gamu ne da takaici anata wasan karkashi jagorancin Andre Villas Boas inda suka tashi babu ci tsakaninsu da Stoke City.

Golan Stoke Asmir Begovic shine hana kwallon John Obi Mikel da Nicolas Anelka ciwa Chelsea kwallo.