Galatasaray na zawarcin Eboue daga Arsenal

ebuoe Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Eboue

Galatasaray ta tabbatar da cewar ta soma tattaunawa don sayen dan kwallon Arsenal Emmanuel Eboue.

Dan kwallon Ivory Coast din mai shekaru 28, ya koma Gunners ne a shekara ta 2005, amma kuma a kakar wasan data wuce sau 13 kacal ya bugawa Kulob din.

Sanarwar da Galatasaray ta fitar ta ce"Mun fara tattaunawa da Arsenal FC dan kwallon Ivory Coast Emmanuel Eboue".

Eboue ya bugawa Arsenal wasanni 216 inda ya zira kwallaye 13 tun zuwansa daga kulob din Beveren dake Belgium shekaru shida da suka wuce.