An nada Van Persie kyaftin din Arsenal

Van Persie
Image caption Robin Van Persie

An nada Robin van Persie a matsayin sabon kyaftin din Arsenal.

Dan kwallon Holland din mai shekaru 28 ya shafe kusan shekaru bakwai tare da kulob din kuma ya maye gurbin Cesc Fabregas wanda ya koma Barcelona a wannan makon.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewar "shine shugabanmu ta hannunsa ne zamu samu nasara".

Mai tsaron baya Thomas Vermaelen shine zai kasance mataimakin Van Persie.

Dan wasan Holland din yace"a matsayin kyaftin din shine jakadan kulob din kuma na san yadda lamarin yake tunda na shafe shekaru goma ina taka leda".

Zai rataya kambun kyaftin a ranar Asabar a wasansu da Liverpool a filin Emirates.