An nemi miliyan 20 kan mahaifin Mikel

John Obi Mikel
Image caption Mikel Obi ya nemi mutanen da su yiwa Allah su saki mahaifin nasa

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce mutanen da suka yi garkuwa da mahaifin shahararren dan kwallon Najeriya da Chelsea wato John Obi Mikel sun nemi da a basu kudin fansa na naira miliyan 20 kafin su sake shi.

Kakakin rudunar 'yan sanda ta jihar Filato, Apev Jacob ya ce sun gano inda aka bar motar mahaifin Mikel, amma bai bada karin haske game da irin tattaunawar da ake yi da wadanda su ka yi garkuwa da shi ba.

Iyalan Mikel din ma sun ki su ce wani abu game da kudin fansan da aka nema.

John Obi Mikel dai na karbar albashi fam dubu dari a kowani mako a kungiyarshi ta Chelsea.

Michael Obi, wanda ke da kamfanin sufurin motoci a birnin Jos, ba a ji duriyarsa ba tun ranar Juma'a.

Amma ranar Talata, wadanda suka sace shi sun tuntubi iyalansa har sau biyu, inda da farko suka shaida musu cewa an fice da Michael daga Jos zuwa birnin Lagos.

A tattaunawa ta biyu da suka yi da mutanen daga bisani, sun gayawa iyalansa inda za su dauki motar da aka kama Michael lokacin da yake barin wurin aiki ranar Juma'a.

Daga bisani an gano motar a birnin Jos, amma iyalan nasa ba su bada karin haske kan inda aka gano motar ba.

Sai dai kwamishinan 'yansanda a jihar ta Plateau Diko Ayeni ya shaida wa BBC cewa suna iya kokarinsu tare da iyalan mutumin domin gano inda ya ke.

"Kawo yanzu ba mu samu wani karin haske kan lamarinba, amma muna aiki tare da iyalan mutumin, kuma babu wanda muka kama".