An gano motar da aka sace baban Mikel Obi

John Obi Mikel
Bayanan hoto,

Mikel Obi ya nemi mutanen da su yiwa Allah su saki mahaifin nasa

Mutanen da suka sace mahaifin dan kwallon Najeriya John Obi Mikel sun tuntubi danginsa a karon farko, sannan an gano motar da aka sace shi a cikinta.

Michael Obi, wanda ke da kamfanin sufurin motoci a birnin Jos, ba a ji duriyarsa ba tun ranar Juma'a.

Amma ranar Talata, wadanda suka sace shi sun tuntubi iyalansa har sau biyu, inda da farko suka shaida musu cewa an fice da Michael daga Jos zuwa birnin Lagos.

Mutanen dai ba su bayyana ko su wanene su ba - kuma ko menene manufarsu - har yanzu ba su gabatar da wata bukata ba, iyalan na sa sun shaidawa 'yansanda halin da ake ciki.

A tattaunawa ta biyu da suka yi da mutanen daga bisani, sun gayawa iyalansa inda za su dauki motar da aka kama Michael lokacin da yake barin wurin aiki ranar Juma'a.

Daga bisani an gano motar a birnin Jos, amma iyalan nasa ba su bada karin haske kan inda aka gano motar ba.

Sai dai kwamishinan 'yansanda a jihar ta Plateau Diko Ayeni ya shaida wa BBC cewa suna iya kokarinsu tare da iyalan mutumin domin gano inda ya ke.

"Kawo yanzu ba mu samu wani karin haske kan lamarinba, amma muna aiki tare da iyalan mutumin, kuma babu wanda muka kama".

Lamarin na baya-bayan nan dai zai iya sanyaya ran dan wasan na Chelsea, wanda danginsa suka gudanar da addu'a ranar Litinin a Jos domin ganin an sako shi.