Vidic zai yi jinya na tsawon makwanni biyar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vidic tare da Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce, kyaftin din kungiyar Nemanja Vidic ba zai taka leda ba na tsawon wata guda bayan raunin da ya samu.

Vidic, mai shekarun haihuwa 29, ya samu rauni ne a wasan da United ta buga da West Brom a ranar lahadin da ta gabata.

A lokacin dai an dauka zai yi jinya ne na tsawon makwanni biyu.

Amma dai Rio Ferdinand, wanda shima ke jinya zai iya dawowa taka leda a karshen watan Agusta.