Villas Boas ya ce ya samu sa'ida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas Boas

Sabon kocin Chelsea, Andre Villas Boas ya ce hankalinsa ya kwanta bayan da Chelsea ta doke West Brom da ci biyu da guda.

A wasan farko da Chelsea ta buga a kakar wasan bana a gasar Premier, ta tashi canjaras ne tsakanin ta da Stoke City.

Villas Boas ya ce baya fuskantar matsin lamba, ko kadan, amma ya nuna kwarin gwiwa cewa kungiyar za ta kara haskaka nan gaba a gasar.

West Brom dai ce ta fara zura kwallon farko a ragar Chelsea, kafin a tafi hutun rabin lokacin, bayan an dawo ne kuma sai Anelka ya farkewa Chelsea, kafin kuma Malouda ya zura ta biyu.