An gano Mahaifin Mikel Obi a Kano

Image caption John Obi Mikel

Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta gano mahaifin John Mikel Obi kwanaki goma sha daya bayan an sace shi a birnin Jos dake jihar Filato.

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Idris, ya shaidawa manema labarai cewa, sun gano shine a jihar ta Kano kuma sun cafke wasu maza biyar da mace guda wanda da ake zargin cewa sun yi garkuwa da shi ne.

Maihaifin Mikel, wato Miicheal Obi ya shaidawa BBC cewa an sace shi daga Jos inda aka wuce da shi Kano.

Micheal Obi dai ya shaidawa BBC cewa ya sha dan karan duka a lokacin da ake tsare da shi

A ranar 12 ga watan Agusta ne dai aka nemi Michael Obi aka rasa a birnin na Jos.