Arsenal da Man City sun cimma yarjejeniya kan Nasri

Image caption Samir Nasri

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta ce ta cimma yarjejeniya da kungiyar Manchester City kan dan wasanta Samir Nasri.

Dan wasan mai shekarun haihuwa haihuwa 24 ya takawa Arsenal leda na tsawon shekaru uku.

A yanzu haka dai Arsenal ta fidda sunan dan wasan daga jerin wadanda za su taka mata leda a wasan share fage na UEFA da Udinese a ranar Laraba.

A yanzu haka dai, za'a duba lafiyar Nasri ne a kungiyar City, sannan a cimma wasu ka'idoji kafin ya koma kungiyar.

Rahotanni dai na nuni da cewa Manchester City ta sayi Nasri ne akan fam miliyan 25.