Mahaifin Mikel Obi ya koma wurin iyalansa

Image caption Mahaifin Mikel Obi, Micheal Obi

Yanzu haka mahaifin dan wasan nan na kungiyar kwallon kafa ta Ingila John Mikel Obi, wanda jami'an tsaro suka kubutar daga hannun mutanen da suka sace shi ya koma gida inda ya sake haduwa da iyalansa. Iyalan nasa dai sun bayyana matukar farin ciki da sake ganin mai gidan nasu, inda suka kuma bayyana cewa zasu kais hi asibiti domin a duba lafiyarsa sakamakon irin rikon da masu garkuwar suka yi masa. Su kuwa 'yan sanda wadanda suka kubutar da dattijon, sun bayyana cewa masu garkuwar a tun farko sun nemi kudin fansa na dala biliyan hudu kafin jami'an tsaro su yi masu dirar mikiya a inda suke garkuwar da shi a Kano.

Shi dai mahifin dan John Mikel Obin, rundunar yasandan Jihar Filato ce ta gabatar da shi a gaban manema labarai a hedikwatarta ta dake birnin Jos inda kwamishinan 'yan sandan jihar Mista Emmanuel Dipo Ayeni, ya yi wa manae ma labaran bayani dalla-dalla yadda suka kai ga nasarar kubutar das hi. Daga bisani kuma rundunar 'yansanan ta mika Pa Mikel Obi ga iyalansa.

Hukumomin yansanda dai sun bayayana cewa bisa irn bayanan da suka samu, masu garkuwar sun azabtar da mahafin John Mikel Obin, ta hanyar yi masa duka da kuma bashi miyagun kwayoyi wadanda suka gusar masa da hankali kana suka shafi yanayin lafiyarsa. Shi dai Pa Mikel Obi, ya shafe kimanin kwanaki goma sha biyu ne a hannun wadanda suka yi garkuwa da shin kuma rundunar yansandan ta ce ta kama mutane shida da take zargi da hannu a lamarin inda kuma take ci gaba da bincike da nufin gurfanar da su a kotu.