Sochaux ta kai karar Newcastle Fifa kan Modibo Maiga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Modibbo Miaga

Kungiyar Sochaux dake Faransa ta bukaci Fifa da ta hana Newcastle tuntubar dan wasan ta Modibo Maiga ba, ba tare da izinin ta ba.

Kungiyar dai ta ce ta hana Newscatle tuntubar dan wasan ta a karo biyu amma abun ya ci tura.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 23 na da sauran shekaru uku a kwantaraginsa da Sochaux, kuma ya zura kwallaye 15 a wasanni 36 da ya buidawa kungiyar a kakar wasan bara.

Dan wasan dai yanzu yaki yayi horo da kungiyarsa, inda yake nema ta siyar da shi ga kungiyar Newcastle.