Samir Nasri ya koma Manchester City

Image caption Samir Nasri

Kungiyar Manchester City ta kammala siyan dan wasan Arsenal Samir Nasri a kan fam miliyan 25.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 24 ya sa hannu ne a kwantaragi na tsawon shekaru hudu.

Nasri dai zai takawa City leda a wasan da kungiyar za ta fafata da Tottenham a ranar lahadi.

Dan wasan dai ya zura kwallaye 15 a kakar wasan bara. Kuma zai sanya rigar kwallon mai lamba 19 ne a Manchester City.