Najeriya ta yunkuro a jerin kasashe da Fifa ta fitar

Image caption Tawagar Super Eagles

Kasar Najeriya dai ta dago sama a jerin kasashen da Fifa ta fitar daga matakin na biyar a nahiyar Afrika zuwa na hudu.

Kasar Ivory Coast dai ce ta daya a nahira Afrika a jerin kasashen da Fifa ta fitar a watan Agusta.

Najeriya dai kuma a duniya ta kara gaba daga matsayin na 43 zuwa 38.

Kasar Algeria ma ta taka rawar gani duk da cewa ta dan jima ba ta buga wasanni ba.

A yanzu haka dai, kasar ta shiga cikin jerin kasashen 50 dake tasiri a harkar kwallon kafa.

Jerin kasashen 10 da Fifa ta fitar na watan Agusta a nahiyar Afrika.

1. Ivory Coast

2. Masar

3. Ghana

4. Najeriya

5. Burkina Faso

6. Algeria

7. Kasar Afrika ta kudu

8. Senegal

9. Kamaru

10. Tunisia