AFC 2013: Kasar Afrika ta kudu ta maye gurbin Libya

Image caption Filin wasa na Rustenburg a kasar Afrika ta kudu

Kasar Afrika ta kudu ta ce itace za ta dauki bakoncin gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2013 a maimakon Libya.

Kasashen biyu dai sun cimma yarjejeniyar musayar daukar bakoncin gasar ne, inda kasar Libya za ta shirya gasar da za'a yi a shekarar 2017.

Kasar Afrika ta kudu dai ce ta bayyana wannan matakin, amma ta ce Hukumar kwallon Afrika ba ta amince da yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma ba.

Akwai shakku cewa Libya ba za ta iya daukar bakoncin gasar 2013 saboda rikicin siyasa da ta barke a kasar.