Bin Hammam ya daukaka kara

Bin Hammam Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bin Hammam ya ce Fifa ba ta yi masa adalci ba

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Asia Mohammed bin Hammam ya daukaka kara kan dakatarwar da Fifa ta yi masa daga harkar kwallo har abada.

Hammam dan kasar Qatar, an dakatar da shi ne bayan da aka same shi da yunkurin bayar da cin hanci.

A wata sanarwa, Bin Hammam, mai shekaru 62, ya ce: "Na mika takardun kara ta ga kwamitin daukaka kara na Fifa.

"Ba na saran za a yi min adalci, amma buri na shi ne na samu damar kaiwa ga babbar kotun da ke shari'a kan wasanni."

Bin Hammam ya zamo jami'in Fifa mafi girma da aka dakatar a shekaru 107 da ta shafe, bayan da aka same shi da yunkurin baiwa jami'an yankin Caribbean cin hanci a kokarinsa na kayar da Sepp Blatter daga shugabancin Fifa.

An zarge shi ne da kokarin sayen kuri'u a zaben shugabancin Fifa da aka yi a watan Yunin da ya gabata.