Daegu: Asafa Powell ba zai yi tsere ba

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Asafa Powell

Dan kasar Jamaica Asafa Powell, ba zai samu tseren mita dari ba, saboda rauni a gasar tsere ta duniya da za'a yi birnin Daegu dake kasar Koriya ta kudu.

Da dai an sa ran cewa dan tseren mai shekarun haihuwa 28 zai kalubalanci Usain Bolt a gasar amma zai ya gaggara murmurewa bayan raunin da ya samu a farkon wannan wata.

Janyewar Powell ta kawo koma bayan kan tseren maza, saboda shima dan kasar Amurka Tyson Gay bazai samu halartar gasar ba, saboda yana fama da rauni.

Har yanzu bai kungiyar Jamaica ba ta bada tabbacin cewa Powell ba zai yi tsere ba.