Osaze ba zai buga wasan Najeriya da Madagascar ba

Image caption Osaze Odemwingie

Dan wasan Najeriya da kungiyar West Brom Peter Odemwingie ya ce ba zai samu buga wasan da Najeriya za ta buga da Madagascar ba saboda yana fama da rauni a gwiwarsa.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 30 ba zai samu buga wasan ba a ranar 4 ga watan Satumba, da kuma wasan sada zumunci da Najeriya za ta buga da Argentina.

Odemwingie ya ce ya fama raunin da ya samu ne a gwiwarsa a wasan da kungiyarshi ta buga da Chelsea a makon daya gabata.

"Gaskiya ban ji dadi ba, an shawarce ni ne da in huta kamar na mako guda. In ji Osaze.

"Na kosa in taimakwa kungiya ta da kasa ta saboda suna matukar bukata ta."

Odemwingie dai bai takawa Najeriya leda ba tun a watan Mayu, a wasan da ta buga da Habasha a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika.