Yaran Ferguson sun tarawa yaran Wenger gajiya

Image caption Rooney ya zura kwallaye uku a wasan

Manchester United ta lallasa Arsenal da ci takwas da biyu a wasan da kungiyoyin suka buga a filin wasa na Old Trafford a gasar Premier ta Ingila.

Welbeck ne ya zura kwallon farko ana minti 22, amma daga baya sai aka fidda shi saboda ya samu rauni. Ashley young ne kuma ya zura ta biyu ana minti 28.

Can kuma ana minti 48 sai Rooney ya zura ta uku a bugun falan daya. An kusan a tashi hutun rabin lokaci ne kuma, Walcott ya fanshewa Arsenal kwallo guda.

Da aka dawo hutun rabin lokaci ne dai Rooney ya zura kwallonsa ta biyu ana minti 64, sannan kuma Nani ya zurawa Manchester kwallo na biyar a minti 67.

Park Ji Sung ne ya zura kwallo ta shida ana minti saba'in a yayinda kuma, Van Persie ya sake fanshewa Arsenal kwallon guda a minti 74.

Rooney ya zura kwallonsa ta uku ne ana minti 82 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Ana cikin karin lokacin ne kuma Ashley Young ya zura kwallo ta takwas.

Arsenal dai ta kammala wasan ne da 'yan wasa goma bayan an sallami Carl Jekinson.