ACN 2012: Har yanzu akwai sauran rina a kaba

ACN 2012: Har yanzu akwai sauran rina a kaba
Image caption A kasar Angola aka gudanar da gasar da ta gabata

A daidai lokacin da ya rage wasanni biyu a kammala gasar share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afrika ta 2012, al'amura sai kara zafafa suke yi.

Kawo yanzu dai kasashe hudu sun riga sun bayyana, inda Botswana - wacce ke halarta a karon farko ta samu shiga tare da Ivory Coast, baya ga masu masaukin baki Equatorial Guinea da Gabon.

Hakazalika kuma, kasashe 25 na fatan samun damar kaiwa ga gaci a gasar wacce za a yi a watan Janairu mai zuwa.

Kasashen 11 da za su zamo kan gaba a rukunansu za su samu shiga gasar kai tsaye, tare da biyun da suka fi taka rawa a mataki na biyu - da kuma kasar da ta zamo ta biyu a rukunin K, wanda shi kadai ne ke da kasashe biyar.

Ga dai wasannin da za a fata kamar haka:

Rukunin A

02-04/09/11: Mali v Cape Verde 02-04/09/11: Zimbabwe v Liberia

Rukunin B

02-04/09/11: Madagascar v Nigeria 02-04/09/11: Guinea v Ethiopia

Rukunin C

02-04/09/11: Libya v Mozambique (za a buga ne a Mali) 02-04/09/11: Comoros v Zambia

Rukunin D

02-04/09/11: Tanzania v Algeria 02-04/09/11: Central African Republic v Morocco

Rukunin E

02-04/09/11: Senegal v DR Congo 02-04/09/11: Cameroon v Mauritius

Rukunin F

02-04/09/11: Namibia v Gambia

Rukunin G

02-04/09/11: Niger v South Africa 02-04/09/11: Sierra Leone v Egypt

Rukunin H

02-04/09/11: Rwanda v Ivory Coast 02-04/09/11: Burundi v Benin

Rukunin I

02-04/09/11: Congo v Sudan 02-04/09/11: Ghana v Swaziland

Rukunin J

02-04/09/11: Kenya v Guinea Bissau 02-04/09/11: Angola v Uganda

Rukunin K

02-04/09/11: Rwanda v Ivory Coast 02-04/09/11: Burundi v Benin